An yanke ma matar da ta caka ma Mijinta wuka, hukuncin kisa ta hanyar rataya

An yanke ma matar da ta caka ma Mijinta wuka, hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wata mata mai suna Victoria Gagariga mai shekaru 33 ta gamu da fushin kotu, bayan Kotun ta kama ta dumu dumu da laifin kisan Mijinta, Henry Gagariga, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Alkalin babbar Kotun jihar Bayelsa, Mai shari’a Nayai Aganaba ne ya yanke wannan hukunci ga Uwargida Vctoria, wanda aka tuhumeta da kashe Maigidanta a ranar 4 ga watan feburairu na shekarar 2015, ta hanyar caka masa wuka a lokacin da yake cikin barci a gidansu dake unguwar Akenfa na jihar Bayelsa.

KU KARANTA: Rikicin Kwankwaso da Ganduje ya ruruta ayyukan yan bangan siyasa a jihar, jama’a sun koka

A yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Aganaba ya bayyana akwai hujjoji kwarara da suka tabbatar Victoria ce ta aikata kisan, don haka ya zama wajibi a gare shi ya yanke mata hukuncin kisa, babu makawa.

An yanke ma matar da ta caka ma Mijinta wuka, hukuncin kisa ta hanyar rataya
Victoria

“Aikina in yanke hukuncin da ya dace da wannan laifi da matar nan da aikata, amma zartar da hukuncin kisan a kanta, hakki ne da ya rataya a kan gwamnan jihar Bayelsa, ina fata zai yi abinda ya dace game da ke.

“A nan na yanke miki hukuncin kisan kai ta hanyar rataya, ina rokon Ubangiji ya yi miki rahama.” Inji Mai shari’a Aganaba.

An yanke ma matar da ta caka ma Mijinta wuka, hukuncin kisa ta hanyar rataya
A baya

A wani labarin kuma, an cigaba da shari’ar matar nan, Maryam Sanda da ta caccaka ma mijinta, Bilyaminu, wuka har sai da yace ga garinku nan, inda a zaman na ranar Talata, Kotu ta hana bada belinta, duk da ikirarin da tayi na cewa tana da ciki, wata uku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng