Wani Fasto ya shiga addinin Musulunci ta dalilin shugaban kasa Muhammadu Buhari

Wani Fasto ya shiga addinin Musulunci ta dalilin shugaban kasa Muhammadu Buhari

Dama Annabi ya yi gaskiya, inda cikin wani hadisi yake fadin mutum zai yi rayuwa cikin kafirci, har sai yana gab da karshen rayuwarsa, sai yayi imani, yayin da wani kuma yana cikin imani har sai yana gab da karshen rayuwarsa, sai ya kafirta.

Tabbas Annabi ya yi gaskiya, inda a nan ma wani Faston cocin Anglican dake garin Shagamu na jihar Ogun ne ya Musulunta, inda a cewarsa ya shiga Musulunci ne ta dalilin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Rikicin Kwankwaso da Ganduje ya ruruta ayyukan yan bangan siyasa a jihar, jama’a sun koka

Jaridar Rariya ta ruwaito Faston mai suna Rabaran Simon Paul yace ya Musulunta ne tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Ingila bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita, duk da irin muguwar addu’ar da suka yi masa a lokacin.

Wani Fasto ya shiga addinin Musulunci ta dalilin shugaban kasa Muhammadu Buhari
Faston

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Simon Paul na fadin: “A lokacin da shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya tafi kasar Ingila don jinyar rashin lafiyar da yake fama da ita, kungiyar kiristocin Najeriya ta tara mu limaman Coci coci, ta umarce mu da yin Azumi da addu’o’I da nufin kada Buhari ya dawo gida da rai.

“Ni kuma na yi alkawarin zan yi addu’a, amma fa idan ya dawo da ransa zan koma Musulunci, kwastam sai ga shi ina kallo a talabijin Muhammadu Buhari ya sauko daga kan jirgi da kansa, lafiyarsa kalau, daga nan na rungumi addinin Musulunci, na canza suna na zuwa Abubakar.” Inji shi.

Sai dai bayan da yan uwansa kiristoci suka samu labarin ficewrsa daga addinin, sai suka fara yi ma rayuwarsa barazana, da nufin hallaka shi, daga na ne ya samfe ya name mafaka a garin Asaba na jihar Delta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng