Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya kaddamar da takararsa ta kujerar Sanata

Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya kaddamar da takararsa ta kujerar Sanata

A ranar Laraba, 7 ga watan Feburairu ne mashawarcin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan al’amuran majalisar wakilai, Honorabul Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila ya kaddamar da takararsa ta neman kujerar Sanata a jihar Kano.

Kawu ya bayyana cewa kwarewarsa da sanin makaman aiki, tare da iya lalubo hanyoyin samar ma matasa ayyukan yi, ka iya bashi damar darewa kujerar Sanatan al’ummar Kano ta kudu, inji rahoton Rariya.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi ma yan ta’addan Boko Haram jini da majina, sun tarwatsa kamfanin ƙera bama bamai

Sai dai majiyar Legit.ng ta gano a yanzu haka Sanata Kabiru Gaya ne ke dafe da wannan kujera, don haka ake ganin akwai kallo a tirka tirkan kwace wannan kujera daga hannunsa,duba da dadewarsa a majalisar dattawan.

Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya kaddamar da takararsa ta kujerar Sanata
Siyasar Kano: Kawu Sumaila

A yayin taron, an jiyo Kawu na wasa kansa da kansa, yana cewa: “Na kwashe shekaru 25 ana damawa da ni a al’amuran siyasa, kuma shekaru na 12 ina wakiltar Sumaila da Takai a majalisar wakilan kasar nan, don haka ina da gogewa a harkokin majalisa.

“Sai da yi addu’o’I tare da istihara kafin na ayyana bukatar tsayawa takarar kujerar nan, kuma kwarin gwiwar da na samu game da hakan ne ya sanya ni tuntuubar jama’an kananan hukumomin Kano ta kudu, kuma Alhamdulillah sun nuna min kauna.” Iniji shi.

Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya kaddamar da takararsa ta kujerar Sanata
Siyasar Kano: Kawu Sumaila

Kawu yace karancin shekarunsa, sun yafi cancanta da kujerar nan, ba kamar Sanata Kabiru gay aba, saboda yana da karfi a jiki, tare da kuzarin lalubo ayyukan cigaba ga al’ummarsa.

Ba’a kammala taron ba, sai da Kawu ya rarraba shanun noma guda 80, tare da tarakta ga shuwagabannin jam’iyyar APC a kananan hukumomi guda 6 dake mazabar tasa, hakazalika ya raba injinan markade, naira dubu 30 ga shuwagabannin mata dake yankin.

Siyasar Kano: Kawu Sumaila ya kaddamar da takararsa ta kujerar Sanata
Shanu

Kawu bai tsaya nan ba, sai da ya raba ma yan takarkarun Ciyamomi na kananan hukumomin naira 200,000, su kuma yan takarar mataimakin shugaban kananan hukumomin sun samu naira 100,00 kowannensu, yayin da su kuma shuwagbannin APC a mazabu suka samu buhunan shinkafa, masara da naira dubu 30, kowannensu.

Da wannan tagomashi da Kawun yayi ma jama’ansa ne ake ganin tabbasa ya shirya tsaf don gwada kwanjinsa da Sanata Kabiru Gaya a siyasar kwatar kujerar mai wakiltan jama’an Kano ta kudu a majalisar dattawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng