Shin garin yaya Shekau yaji wuta ya nuna gajiyawar shi a fili?

Shin garin yaya Shekau yaji wuta ya nuna gajiyawar shi a fili?

- Shekau ya ce mutuwar sa ita ce ta fi mashi da irin wannan masifar da yake ciki

- Ya bukaci mutanen sa dasu tashi tsaye domin daukaka kalmar Allah

- Ya karyata ikirarin da sojojin Najeriya keyi na cewar sun karbe dajin Sambisa daga hannun su

Boko Haram: Shekau yaji wuta ya nuna gajiyawar shi a fili
Boko Haram: Shekau yaji wuta ya nuna gajiyawar shi a fili

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, a sabon bidiyon da ya fitar da harshen Hausa, ya ce ya gaji da wannan tashin hankalin dake addabar su. "Na gaji da wannan masifar, gwanda na mutu na shiga aljanna kawai".

A cikin bidiyon Shekau ya kasa boye damuwar shi, akan harin da ake kawo musu, da kuma asarar mutanen sa da yake ta faman yi. Cikin murya mai ban tausayi, Shekau ya roki magoya bayan sa dasu dauki makamai su cigaba da taimaka masa da kai hare - hare, har lokacin da rayuwar shi zata zo karshe.

Shugaban 'yan ta'addan, ya ce da'awar da sojojin Najeriya suke na cewar sun gudu daga dajin Sambisa soki burutsu ne kawai da karya. Ya bayyana cewar har yanzu yana cikin dajin, kuma komai yana tafiya yanda ya kamata. Ya ce mutanen shi zasu cigaba da kai hare - hare, duk da cewar kasar Kamaru ta fara turo sojojin ta cikin yakin.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tace kimanin mutane miliyan bakwai ke amfana da tsarin samar da aikin yi

A kasa wasikar da Shekau ya rubuta ce.

"Ba ni da wani sako da ya wuce batun bauta wa Allah shi kadai, ba tare da nuna gajiya wa ba. Ba kamar daya daga cikin shugabannin kafirai, wanda yake kama da gwaggwon biri, wanda yake alfaharin cewar sun kafa rundunar hadin gwiwa tare da sojojin Kamaru, domin yakar mu.

"Hadda cewa ba wai a iya daji Sambisa zasu yake mu ba hadda duk wani lungu da sako na kasar nan. Don haka ina bayyana muku cewar muma bamu son ganin kowanne dan Najeriya, Kamaru, Chadi, har ma da Benin, saboda haka ina kira ga mutanen mu da suke Abuja, Legas, Benin, Kaduna da duk wani sako na kasar nan, idan ku ka sami dan Najeriya ku tabbatar da cewar kun kashe shi, idan har baya nuna goyon baya a gare mu; amma idan bashi da ilimi akan da'awar mu to kuyi kokari ku jawo shi cikin mu.

Wannan shine sakon mu na farko. "Sako na biyu shine ku kashe duk wani mutum da yake da'awar cewar Najeriya kasar shi ce, da duk wani wanda yake da niyyar taimakawa Najeriya shima ku kashe shi. Duk wani wanda yake da'awar yada karatun boko shima makiyin mu ne. Da kuma duk wani wanda baya bin sunnar Manzon mu Annabi Muhammadu (S.A.W), da kuma sunnar Sahabban sa, ya kamata ya san cewar shi abokin gabar mu ne, kuma idan ya tare mu sai mun ga bayan shi. A wannan da'awar da muke babu gudu babu ja da baya, kuma muna rokon Allah ya dauki ranmu muna kan yin wannan da'awar. Allah ya bamu sa'a.

"Ya ku 'yan Najeriya musamman ma matasa, da kuke tada jijiyar wuya kuke dakko makamai domin yakar mu, zamu yake ku muma, bamu damu da zigar da ake yi muku ba. Kamar yadda kuka ce baku son ganin mu a Najeriya, haka muma bamu son ganin ku a dajin Sambisa. Sannan kuma shugabannin ku, suma baza su samu zaman lafiya ba, kamar yanda muma baku bar mu mun zauna lafiya ba.

"Sannan kuma kai Janar Roger kai da kake jagorantar sojoji, da har kake alfaharin cewar kun kwace Sambisa, sannan kun ceto wasu mata, mai yasa kuka kasa ceto 'yar sandar da muka sace? kai makaryaci ne, kuna ta yaudaran mutanen ku da motocin da muka kwace a wurin ku, muka bar su sama da shekaru 3 da suka wuce, sannan kuna da'awar cewar kun kashe mu, mai yasa har yanzu muke a raye?

"ya ku 'yan uwa masu tsoron Allah, ku tashi kuyi yaki domin Allah, idan baza ku iya yakar su daga nan ba, ku dawo nan wurin mu, mu hadu mu yake su gaba daya. Ku sani cewar duk wanda ya mutu ba akan tafarkin Allah da manzo ba to wuta ce makomar shi.

Duk inda kuke, koda kuwa a kasar saudiyya ne, matukar akwai makami a hannun ka to ku tashi kuyi yaki domin Allah, ku kashe kowane mutukar baya bin da'awar da muke.

"Wannan shine sakona a gare ku. Nine Abubakar Shekau, wanda ya gagare ku kama wa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel