Sojojin Najeriya sun yi ma yan ta’addan Boko Haram jini da majina, sun tarwatsa kamfanin ƙera bama bamai
Rundunar Sojin Najeriya na sama da na kasa sun samu galaba a kan yan ta’addan Boko Haram a wani sabon yunkuri da Sojojin suka kaddamar da kakkabe ragowar yan ta’addan a jihar Borno.
Mataikamakin daraktan watsa labaru na yaki da ta’addanci, kanal Onyeama Nwachukwu ne ya bayyana hake cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 7 ga watan Feburairu, inda yace kimanin sati hudu kenan Sojojin na gallaza ma yan Boko Haram a dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi.
KU KARANTA: Wani abin takaici ya faru a jihar Katsina, gardawa guda 7 sun fyadeɗ yarinya mai shekaru 14
Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata 6 ga watan Feburairu hadakan Sojojin sama da na kasa sun kai wani samame zuwa wani sanannen sansanin yan Boko Haram mai suna ‘Camp Zairo’, inda suka yi ma yan ta’addan kaca kaca, tare da tarwatsa kamfanin da suke hada bama bamai.
Sojojin sun gano kwanukan iskar gas guda 88, na’urar kwamfuta guda 1, wayoyin sadarwa guda 2, Babura guda 22, kekuna 18, kayan abinci da sauran kayayyakin amfaninsu na yau da kullum.
Daga karshe sanarwar ta kara da cewa Sojojin Najeriya a shirye suke su bada gudunmuwarsu na ganin sun tabbatar zaman lafiya a Najeriya tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, ta hanyar kakkabe abinda ya ragu na yan ta’addan Boko Haram.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng