Majalissar Wakillai ta bukaci Buhari ya tsige Sifeto janar ‘yansanda
- Majalissa ta nemi shugaban Buhari ya sauke Ibrahim Idris daga mukamain shugaban 'yansandan Najeriya
- Majalissar wakillai ta ce shugaban kasa ya maye gurbin sifetan jana na 'yansanda da kwararren jami'in dansanda
Majalissar wakillai, ta yi kira da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ya gaggauta sauke Sifeto Janar na ‘yansanda, Ibrahim Idris, a ranar Laraba.
Majalissar ta yi wannan kiran ne a yayin da suke zaman zauren majalissa a ranar Laraba, inda suka Bukaci shugaban kasa, ya maye gurbin shi da kwararren jami’in dansanda.
Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito labarin da Majalisar Wakilai ta umurci Sifeta Ibrahim Idris ya roki gafarar Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, bisa ikakarin sa na cewa Ortom mutum ya gaza a bakin aikin sa.
KU KARANTA : Kotu ta sake hana belin Maryam Sanda
Ta yi wannan umurni ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabarairu bayan kwamitin kula da Lamurran Hukumar 'Yan Sanda na Majalisar ta gabatar da sakamakon binciken ta ga Majalisar.
Mafi akasarin 'Yan Majalisar sun yi tir da wannan furuci na Sifetan. Majalisar ta kuma bukaci a sauke Mashood Jimoh a matsayin sa na mai magana da yawun Hukumar, don ta bakin sa ne furucin ya fito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng