Yanzu Yanzu: Rundunar yan sandan Najeriya ta fara diban ma’aikata na 2018, tace shirin kyauta ne
Rundunar yan sandan Najeriya ta fara shirin daukar ma’aikata na 2018 yayinda hukumar ta yi gargadin cewa kada wanda ya biya ko sisi yayin neman aikin.
A wata yar gajeriyar sako a shafukan zumunta da safiyar ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, hukumar tace: "Rundunar yan ssandan Najeriya na gayyatan masu neman aiki daga yan Najeriya a hukumar ta.”
Ta bukaci jama’a das u duba cikakkun bayanai na tallar wannan aiki a shafukan jaridu na yau Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2018.
Jaridar Leadership – Shafi na 33
Jaridar Daily Trust - Shafi na 11
Jaridar The Nation - Shafi na 45
Jaridar Daily Sun - Shafi na 8
“Za a rufe karban takardu makonni shida daga ranar da aka fara tallatawa,” Inji dan guntun sanarwan.
KU KARANTA KUMA: Sanata ya tallafawa al’umman mazabar shi da kwaskon suya (hotuna)
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Majalisar Dattijai ta bukaci a mai da kowane Dan sanda zuwa jihar sa ta haihuwa, daga kan mukamin Sufeto zuwa Kurtu, saboda magance matsalar tsaro a kasar nan.
Kudurin ya biyo, bayan da Sanata Ademola Adeleke, na jihar Osun ya bukaci da a mai da kananan ma'aikatan 'yan sandan zuwa garuruwan su na haihuwa, don bunkusa aikin tsaro.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng