'Sojoji na kuntatawa mutane a kudancin Kamaru'

'Sojoji na kuntatawa mutane a kudancin Kamaru'

- Mutanen yankin dake amfani da harshen turanci a kasar Kamaru suna kwarara a Najeriya dan neman mafaka daga cin zarafin su da sojoji kasar ke musu

- Majalissar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin cewa za a sami karin dubban 'yan gudun hijira da za su shigo kasar Najeriya daga Kamaru idan rikicin ya ci gaba

Ana zaman tsoro a yankin dake amfani da harshen Turanci a kasar Kamaru bayan dakarun sojoji sun far musu da sunan farautar ‘yan aware.

Wani dan majalissa daga garin Batibo ya zargi sojojin da cin zarafin mutanen wurin tare da kwace musu kudaden wanda yasa waus na guduwa daga gidajen su.

Mutanen yanki suna cigaba da kwarara zuwa garuruwan Najeriya dake kan iyaka da kamaru, dan neman mafaka.

'Sojoji na kuntatawa mutane a kudancin Kamaru'
'Sojoji na kuntatawa mutane a kudancin Kamaru'

Masharhanta dai na ganin rashin tausayin da sojojin ke nuna wa mutanen yankin dake amfani da harshen Turanci na iya tunzura mutane ga fafutikar neman ballewa daga kasar.

KU KARANTA : Rikicin Benuwe : IG ya tura rundunonin ‘yansada na musamman jihar Bneuwe

A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta mika wa hukumomin Kamaru shugabannin 'yan a waren da suka zo neman mafaka a Najeriya, matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da shi.

Hukumomin agaji a Najeriya sun ce 'yan gudun hijira fiye da 40,000 ne suka shiga kasar daga yankin da ke magana da harshen Turanci a Kamaru, kuma adadin na ci gaba da karuwa.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadi da cewa za a samu karin dubban 'yan gudun hijira da za su shigo kasar Najeriya daga Kamaru idan rikicin ya ci gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng