Yadda shugaba Buhari yayi arangama da dubban magoya bayan sa a jihar Nasarawa
- Yadda shugaba Buhari yayi arangama da dubban magoya bayan sa a jihar Nasarawa
- Ya kai ziyarar wuni daya jihar Nasarawa a garin lafiya dake makwaftaka da garin Abuja
Hakika shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na daya daga cikin mutane masu farin jini sosai a tarihin shugabannin da suka taba mulkar talakawan Najeriya.
Wannan ma dai ya kara tabbata biyo bayan irin cincirindon jama'a dubbai da suka fito kwansu-da-kwalkwata domin tarbar sa yayin wata ziyarar wuni daya da yakai jihar Nasarawa a garin lafiya dake makwaftaka da garin Abuja.
KU KARANTA: Limamin coci ya ce Buhari ya je gida ya huta
Legit.ng ta samu dai cewa shugaban kasar ya je ne jihar inda ya kuma kaddamar da wasu manyan ayyukan raya kasa da kuma jin dadin talakawa wanda gwamnan jihar Alhaji Tanko Almakura ya aiwatar.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ribas dake a kudu-maso-kudancin Najeriya Mista Nyeson Wike ya bayyana cewa tabbas jam'iyyar adawa ta PDP ce zata fatattaki shugaba Buhari zuwa garin sa Daura a zaben 2019 da za'a gudanar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala taron kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta PDP da ya samu halartar jiga-jigan jam'iyyar a garin Asaba, jihar Delta da yake zantawa da manema labarai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng