Ziyarar Nasarawa: Yadda Gwamna Almakura ya sha ruwan yabo a wurin Buhari

Ziyarar Nasarawa: Yadda Gwamna Almakura ya sha ruwan yabo a wurin Buhari

- Gwamna Almakura ya sha ruwan yabo a wurin Buhari

- Akalla jami'an tsaro 10,000 ne suka baiwa Buhari kariya

- Sun hada da dogarawan hanya, 'yan sanda, sojoji, 'yan sandan fari da bakin kaya, jami'an shige-da-fice

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa Gwamnan jihar Nasarawa bisa ga ayuukan alherin da ya shimida a jihar sa domin anfanin talakawa yayin da yaje ziyarar wuni daya a jihar ta sa.

Haka nan kuma shugaban kasar ya jinjinawa yan jihar wadanda ya kira yan halak da suka marawa manufofin canji tun kafin ma kafuwar gwamnatin tarayya ta jam'iyyar APC a 2015.

Haka zalika ma Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu, akalla jami'an tsaro sama da 10,000 ne da suka hada da dogarawan hanya, 'yan sanda, sojoji, 'yan sandan fari da bakin kaya, jami'an shige-da-fice da kuma jami'an tsaron farar hula ne suka baiwa shugaban kasa kariya a yayin zuwan sa garin Lafiya, jihar Nasarawa, jiya.

Ziyarar Nasarawa: Akalla jami'an tsaro 10,000 ne suka baiwa Buhari kariya
Ziyarar Nasarawa: Akalla jami'an tsaro 10,000 ne suka baiwa Buhari kariya

KU KARANTA: Atiku na cigaba da kamfe din sa a kasar Inyamurai

Mun samu dai cewa wakilin majiyar mu da ya zagaya manyan tituna da kuma biranen garin ya ga jami'an tsaro a dukkan lungu da sakon garin dake zaman babban birnin jihar sannan kuma wasu na ta sintiri.

A wani labarin kuma, Hakika shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na daya daga cikin mutane masu farin jini sosai a tarihin shugabannin da suka taba mulkar talakawan Najeriya.

Wannan ma dai ya kara tabbata biyo bayan irin cincirindon jama'a dubbai da suka fito kwansu-da-kwalkwata domin tarbar sa yayin wata ziyarar wuni daya da yakai jihar Nasarawa a garin lafiya dake makwaftaka da garin Abuja.

Legit.ng ta samu dai cewa shugaban kasar ya je ne jihar inda ya kuma kaddamar da wasu manyan ayyukan raya kasa da kuma jin dadin talakawa wanda gwamnan jihar Alhaji Tanko Almakura ya aiwatar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng