Son maso wani, ƙoshin wahala: Wani Saurayi ya kiɗime yayin samun labarin auren ɗiyar Dangote

Son maso wani, ƙoshin wahala: Wani Saurayi ya kiɗime yayin samun labarin auren ɗiyar Dangote

- Diyar Dangote, Fatima za ta auri yaron tsohon sufeta janar na Yansanda

- Wani 'Masoyinta' ya nuna damuwarsa da auren

Cikin raha, wani ma’abocin kafar sadarwa zamani, Facebook, Rabiu Biyora ya bayyana halin dimuwa da ya shiga sakamakon labarin auren diyar attajiri Aliko Dangote da za’a yi, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Shi dai wannan matashi ya bayyana cewa ya dade yana kaunar Fatima Dangote tun ba yanzu ba, amma kwatsam sai ji yayi za ta amarce da yaron tsohon sufeta janar na Yansanda, Muhammed Abubakar, Jamilu.

KU KARANTA: Wata ɗalibar jami’ar Ahmadu Bello ta hallaka kanta har lahira a tafkin Tamburawa

Biyora yace: “Haba Fatima Dangote ya zakiyimun haka, kin san dai yadda zuciyata ta tafi a kaunarki, tunani na naki ne, kirjina cike yake da beginki, Na gama shiryawa tsaf, ina jiran inji kin fitar dani a matsayin Ango, kawai sai naji labarin kin zabi wani daban. Na dade ina sanar dake cewa idan ba keba sai dai rijiya amma duk da haka kika zabi wani kika kyaleni.”

Son maso wani, ƙoshin wahala: Wani Saurayi ya kiɗime yayin samun labarin auren ɗiyar Dangote
Biyora da Fatima Dangote

Daga karshe ya bukaci jama’a su kawo masa dauki, idan ba haka ba kuwa zai tunjuma cikin rijiya, amma fa duk a cikin raha da nishadi yake bayyana labarin nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng