Wata ɗalibar jami’ar Ahmadu Bello ta hallaka kanta har lahira a tafkin Tamburawa
Ruwan tafkin Tamburawa na jihar Kano ya ci wata budurwa mai suna Zubaida Nuhu, dalibar a jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria na jihar Kaduna, inji rahoton Premium Times Hausa.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Asabar 3 ga watan Feburairu, inda aka tsinci gawar Zainab Nuhu, wanda daliba ce mai karatun digiri na biyu a fannin albarkatun ruwa.
KU KARANTA: Kwastam ta cafke kwalaben barasa guda 6,444 tare da motocin naira biliyan 1.4 (Hotuna)
Rahotanni daga majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewa budurwar ta fada cikin tafkin ne da nufin kashe kanta, kamar yadda wani shaidan gani da idanu ya tabbatar.
Shaidan mai suna Ibrahim Musa ya bayyana cewar da fari sai da budurwar ta tambayi ma’aikatan dake diban yashi a bakin tafkin cewa wai wani sashin tafkin ne yafi zurfi, daga nan kuma basu sake ganinta ba sai dai gawarta da aka ciro.
Dan uwan mahaifiyar Zainab, mai suna Tajudeen Alhaji ya bayyana cewa Zainaba ta fita gida ne a ranar Asabar din aka tsinci gawarta, da nufin za ta je banki don cire kudin da za ta yi amfani da su a yayin tafiyar da za tayi zuwa Zaria.
“Da misalin karfe 11 na safiyar ranar Asabar ta fita, da nufin zata ke banki ta cire kudi don harkar karatunta a Zaria, amma fitar ta ke da wuya, sai ta aiko ma uwata Jakarta da kuma wayarta. Ni kuma da misalign karfe 4 na yamma ne mahaifiyar ta kira ni cewa Zainab fa bata dawo ba.” Inji shi.
Daga nan ne fa Malam Tajudeen ya sanar ma Yansanda bacewar Zainab da kuma gidajen rediyo don cigiyarta. Sai dai har zuwa lokacin da aka kawo gawar Zainab an rasa takamaimen abinda ya kai ta ga halaka kanta.
Dama dai wani rahoto na babban bankin duniya ya nuna cewar ana samun mutum guda a cikin duk mutanen Najeriya guda biyar da ke fama da matsananciyar damuwa da ka iya kais hi ga halaka.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng