Son zuciya, ɓacin zuciya: Matasa masu budurwar zuciya sun gamu da mummunan hukunci

Son zuciya, ɓacin zuciya: Matasa masu budurwar zuciya sun gamu da mummunan hukunci

Wata kotun majistri ta aika da wasu matasa su uku zuwa gidan kaso biyo bayan kama su da ta yi da laifin balle wani shago tare da afkawa ciki, kuma suka saci kayan abinci da suka kai naira 167,000.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito matasan sun hada da Taoheeb Lamidi, Saheed Sikiru da Imole Adeleye dukkaninsu masu shekaru 20 da haihuwa, amsa laifin da ake tuhumarsu a kai.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya tada jijiyar wuya a majalisa bisa watsi da aka yi da mutanen aka kai ma hari a Birnin Gwari

Dansanda mai kara, Inspekta Samad Aliui ya shaida ma kotu cewa a ranar 30 ga watan Janairu ne matasan suka aikata wannan ta’asa a wani gida dake titin Farajimi, unguwar Agodi na garin Ibadan, da misalign karfe 1 na dare.

Matasan sun saci buhunan shinkafa, giya, kayan shayi da kuma mangyada, da darajarsu ta kai N167,000, wanda yace laifin ya saba ma sasshi na 390 (9), da sashi na 413 da 516 na kundin hukunta manyan laifuka.

Da take yanke hukunci, Alkai Kehinde Omotosho ta yanke musu hukunci zaman gidan shekara 9, inda ta kara da cewa: “Na fahimci barayin nan sun shirya sosai kafin aikata laifin, don a ganinsu ma sun samu nasara, abin takaici ne ace matasa majiya karfi da ya kamata suna taimakon kasa amma ace suna sata.”

Daga karshe ta ce zasu yi zaman kurkukun tare da horo mai tsanani, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

A wani labarin kuma, wata kotun magistri a jihar Legas ta bada umarnin garkame mata wani matashi mai shekaru 25 da ake zargi da hallaka abokin fadansa ta hanyar caccaka masa kwalba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng