Wani matashi ya hau dokin zuciya ya caka ma wani mutumi wuka, ya gamu da fushin Kotu
Wata kotun majistri dake unguwar Ebute Meta na jihar Legas ta bada umarnin garkame mata wani matashi mai suna Femi Olatunji, mai shekaru 25 biyo bayan zarginsa da ake yi da kashe wani da wuka.
Ana zargin wannan matashi da hallaka Fatai Taoreed a ranar 15 ga watan Janairu da misalign karfe 4.20 na rana, kamar yadda dansanda mai kara ASP C. Olagbayi ya bayyana ma Kotu.
KU KARANTA: Yaron Dahiru Bauchi ya kafirta duk wanda yace Shehu Tijjani Allah ne
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito ASP na fadin matashin ya aikata wannan aika aika ne a tashar Aradagun dake garin Badagry, inda ya fasa kwalba, ya caka ma mamacin a hannunsa, nan da nan jinni ya yanke masa, sai mutuwa.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito ASP yace laifin ya saba ma sashi na 222 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Legas, kuma hukuncin kisa ne ya dace ga duk wanda kotu ta tabbatar masa da laifin.
Daga karshe Alkali A.S Salawu ta bukaci a dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Maris, kafin nan babban jami’in jihar mai shigar da kara ya bada shawarar da ta dace da shari’ar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng