Ministan Buhari ya sayi dukiyar naira miliyan 280m a Abuja

Ministan Buhari ya sayi dukiyar naira miliyan 280m a Abuja

- Ministan shugaba Buhari ya sayi katafaren gida mai tsada a birnin Abuja

- Ministan Buhari ya ce da bashin banki ya sayi katafaren gida a Abuja

Wani minista a gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sayi wani katafaren gidan a birnin tarayya Abuja wanda farashin ya kai naira miliyan N280m.

Legit.ng ta samu rahoton cewa a shekara 2017 ministan ya sayi gidan, amma fadar shugaban kasa ta gayyace shi ya zo yayi bayyanin yadda ya samu kudin da ya sayi gidan a lokacin da ta samu labarin cnikin gidan.

Wani majiya mai karfi, ya ce a shekarun baya ministan yana zama a gidan haya da gwamnatin tarayya ta kama masa a shekara 2015, wanda ake biyan naira miliyan N8m a kowani shekara, kafin ya tashi ya koma katafaren gidan da ya saya.

Ministan Buhari ya sayi dukiyar naira miliyan 280m a Abuja
Ministan Buhari ya sayi dukiyar naira miliyan 280m a Abuja

Ministan ya fadawa fadar shugaban kasa cewa, da bashin banki ya sayi gidan kuma sun yi yarjejeniya zai rika biyan su ne da albashin sa, amma fadar shugaban kasa bata gamsu da jawabin sa ba.

KU KARANTA : 'Yan Najeriya miliyan 152 suna rayuwa kasa da $2 a kowani rana - AFDB

Tambaya anan shine? har yaushe zai iya biyan bankin bashin ta da ya ciwa, saboda albashin minista bai kai naira miliyan daya a wata ba.

Kuma ko da zai tara duka albashin sa na tsawon shekaru hudu da zai yi akan kujeran minista ba zai ishe shi ya biya bashin ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng