Bani da laifi, amma zan bari a dama dani – Kakakin IBB
- Mai magana da yawun Ibrahim Babangida, Kasim Afigbua, ya mayar da martani ga farautar shi da rundunar yan sanda ke yi
- Afegbua ya cigaba da cewa shi ba mai laifi bane, amman ya bayyana cewa zai gurfanar da kansa ga hukumomi a ranar Laraba
- Har ila yau lauyoyinsa sun bayyana cewa bai aikata kowane laifi ba, da kuma zargin cewa ana kokarin razana shi don mika kansa
Jaridar Prremium Times ta rahoto cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, Kasim Afegbua, ya wanke kansa daga laifuffuka, bayan farautar shi da rundunar yan sanda ta sanar da cdewan tana yi.
Afegbua wanda ya bayyana cewa a shirye yake don kare kansa a kotu, duk da haka, ya bayyana cewa zai gurfanar da kansa ga hukumomi a ranar 7 ga watan Fabreru.
Legit.ng ta tattaro cewa bayan rahotanni da suka nuna cewa an kama shi, Afegbua a ranar Litinin, 5 ga watan Fabreru, ya bayyana cewa hukumar yan sanda bata gayyace shi ba.
Afegbua ya gabatar da jawabai a daren Lahadi, 4 ga watan Fabreru, inda ya sanar da cewa Babangida ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari sannan ya shawarci yan Najeriya akan hanyar cigaba.
Duk da haka, a jawabai da ya biyo bayan yan sa’o’i wanda ya ci karo da jawabansa, wanda ake zatton tsohion shugaban kasan da sa hannu.
KU KARANTA KUMA: Duk da sabanin dake tsakaninsa da magajinsa, Kwankwaso na nan a APC – Inji Dabo
Al’amarin ya janyo hankulan jama’a; da rahotanni da suka bayyana a ranar Lahadi, cewa hukumar yan sanda na farautan Afegbua.
Jin kadan bayan hukumar yan sandan ta bayyana cewa tana farautarsa, lauyoyin Afegbua sun wanke mai magana da yawun tshohon shugaban kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng