Kasashe biyar sun kulla yarjejeniyar jiragen sama da shugaba Buhari

Kasashe biyar sun kulla yarjejeniyar jiragen sama da shugaba Buhari

A ranar Litinin din da ta gabata ne, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ƙulla wata yarjejeniya ta harkokin jiragen sama da ƙasashe ketare biyar da suka hadar da; Algeria, Congo, Sin, Qatar da kuma Singapore.

Babban hadimin shugaban ƙasar akan hulda da manema labarai, Mallam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan a wata ganawa da 'yan jarida a fadar shugaban dake babban birnin ƙasar nan.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

Mallam Garba yake cewa, shugaban ƙasar ya rattaba hannu akan wannan yarjejeniya bayan amincewar majalisar sa da aka saba gudanar da zaman ta a kowane mako.

KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Nasarawa

Ya ƙara da cewa, wannan yarjejeniya za ta bai wa harkokin jiragen sama na Najeriya da sauran ƙasashen wata dama ta ci gaba mai matuƙar muhimmanci.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya dirra a babban birnin Lafia na jihar Nasarawa, wajen ziyarar aiki ta kwana daya da ya kai domin ƙaddamar da wasu aikace-aikace da gwamnatin jihar ta aiwatar ƙarƙashin jagorancin gwamna Umaru Tanko Al-Makura.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng