Kasar Pakistan shirye take da baiwa Najeriya kyautan makamai - Jakada

Kasar Pakistan shirye take da baiwa Najeriya kyautan makamai - Jakada

A wani hira da jaridar The Nation tayi da jakadan kasar Pakistan zuwa Najeriya, Asim Ali Khan, yayi jawabai iri-iri da shafi alaka da hadin kan kasan Pakistan da Najeriya.

Mr. Asim Ali Khan ya bayyana cewa kasarsa na shirye da taimakawa Najeriya da makamai kyauta domin yakan ta'addanci a Najeriya.

Yace: "Shirye muke da bayar da gudunmuwan da zamu iya badawa na makamai da kayayyakin yaki da horo ga gwamnatin Najeriya, saboda kyakkyawan alakar da ke tsakanimu na diflomasiyya da kuma karfin soja.

Bizan kasuwancinmu da Najeriya ya karu da kashi 26 cikin 100 kuma kasuwanci ya karu da kashi 46 cikin 100 sabanin bara."

Kasar Pakistan shirye take da baiwa Najeriya kyautan makamai
Kasar Pakistan shirye take da baiwa Najeriya kyautan makamai

Yayinda aka tambayeshi kan me kasar ke tunanin zai karfafa alaka tsakanin kasashen guda 2, Asim Ali yace: " Kasar Pakistan ta fara shigarda iskar gas din Najeriya kasarta, kana kuma Najeriya na iya amfana da kamfanonin kasar Pakistan."

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta dauki bokaye aiki

Kwanakin baya, jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa jam'ian sojin kasan Pakistan sun kawo ziyara Najeriya domin hadaka da jami'an sojin Najeriya wajen horo da raba ilimi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng