Babban Bankin kasa (CBN) ya zuba miliyan $210m a kasuwar hada-hadar canjin kudi

Babban Bankin kasa (CBN) ya zuba miliyan $210m a kasuwar hada-hadar canjin kudi

- Babban Bankin kasa (CBN) ya malalo miliyoyin dalar Amurka har $210 a kasuwar hada-hadar canjin kudi

- Darektan sashen sadarwa na CBN, Mista Isaac Okorafor, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya, Litinin

- Ya ce CBN na dauka matakan saukaka tsadar da kudaden ketare ke yi domin bunkasa kasuwanci

Babban Bankin kasa (CBN) ya sanar da cewar ya malalo dala miliyan $210 cikin kasuwar hada-hadar canjin kudi tsakanin bankunan kasar nan domin saukaka harkokin kasuwanci.

Babban Bankin kasa (CBN) ya zuba miliyan $210m a kasuwar hada-hadar canjin kudi
Gwamnan Babban Bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele
Asali: Depositphotos

Da yake bayyana yadda babban bankin ya kasafta kudaden, darektan sashen sadarwa na CBN, Mista Isaac Okorafor, ya ce Dala miliyan $100m za a yi amfani da ita wajen tallafawa manyan masana'antu, yayin da aka ware Dala miliyan $55 domin matsakaita da kananan masana'antu, sai kuma kuma dalibai da masu bukata ta musamman da aka ware wa Dala miliyan $55 su ma.

DUBA WANNAN: Gwamna ya bukaci Buhari ya kafa cibiyar gyaran tunanin masu cin hanci

Kazalika ya tabbatar wa jama'a cewar bankin CBN zai ci gaba da bayar da tallafi a bangaren hada-hadar canjin kudi tsakanin bankunan kasar nan domin samun daidaito da saukin yin kasuwanci.

Ya kara da cewar matakan da CBN din ke dauka na biyan bukata kamar yadda masu shigo da kaya zasu iya tabbatar wa.

A satin da ya gabata Legit.ng ta kawo maku rahoton cewar Naira na kara samun tagomashi a kan Dalar Amurka, Wanda kuma har yanzu tana ci gaba da farfadowa. Ana sayar da Dalar Amurka a kan N360 a kasuwar canjin kudade.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng