Jagoran almajiran Zakzaky na jihar Sokoto ya rasu sakamakon harbin bindiga
- Jagoran almajiran Zakzaky na jihar Sokoto ya rasu sakamakon harbin bindiga
- Malam Kasim Umar ya rasu ne kamar yadda muka samu a jiya, ranar Litinin 5 ga watan Fabrairun
- Malamin ya rasu ne a sakamakon harbin sa 'yan sandan Najeriya suka yi da bindiga a kafar
Labarin da muke samu sun tabbatar mana da cewa shugaban kungiyar nan ta almajiran Malam Ibrahim Zakzaky kuma mabiya mazhabar shi'a ta Najeriya reshen jihar Sakkwato dake a arewa maso yammacin Najeriya ya rasu.
KU KARANTA: Boko Haram: Sanata ya karyata ministan tsaro
Jagoran mai suna Malam Kasim Umar ya rasu ne kamar yadda muka samu a jiya, ranar Litinin 5 ga watan Fabrairun shekara ta 2018 a garin na Sakkwato, in ji mai magana da yawun kungiyar Malam Ibrahim Musa.
Legit.ng dai haka zalika ta samu cewa Malamin ya rasu ne a sakamakon harbin sa 'yan sandan Najeriya suka yi da bindiga a kafar sa yayin da 'yan sandan suka tarwatsa su sa'adda 'yan kungiyar suka yi wata zanga-zanga kin jinin gwamnati tare da halin da shugaban nasu na kasa Malam Ibrahim Zakzaky ya shiga a watan jiya ranar tara ga watan Janairu.
Haka zalika Legit.ng ta tattaro cewa babban malamin ya kwashe sama da shekaru akalla sama da 20 yana shugabantar yan shi'ar a birnin Sakkwato da ke da karancin mabiya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng