Kotu ta kwace £578,080 daga wani kamfani ta ba gwamnatin tarayya
- Kotu ta kwace £578,080 daga wani kamfani ta ba gwamnatin tarayya
- Wannan dai na kunshe ne a cikin wani hukunci da alkalin kotun Mai Shari'a Salisu Saidu ya yi
Wata kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Legas a jiya Litinin ta umurci wani kamfanin dake tu'ammali da harkokin teku watau ZAL Marine Limited da ya bai wa gwamnatin tarayya adadin makudan kudaden da suka kai £578,080 dake ajeye a bankin Diamond.
KU KARANTA: Maryam Sanda da dauke da ciki wata 3
Wannan dai na kunshe ne a cikin wani hukunci da alkalin kotun Mai Shari'a Salisu Saidu ya yi biyo bayan karar da hukumar EFCC ta shigar inda ta zargi kamfanin da karkatar da kudaden na gwamnatin tarayya da kamfanin yayai.
Legit.ng ta samu dai cewa Lauyan hukumar ta EFCC mai suna Mista Rotimi Oyedepo ya bukaci alkalin tun farko dai da ya ba kamfanin umurnin ya maidawa gwamnatin tarayya kudin.
A wani labarin kuma, Mahukunta na hukumar tarayyar kasashen turai a jiya Alhamis sun amince da baiwa kasar Najeriya tallafin akalla Euro 26.5 miliyan a matsayin kudin tallafi domin gudanar da zabukan 2019 cikin mafi kyawon tsari da kuma tsafta da inganci.
Ambasadan tarayyar a Najeriya da kuma tarayyar kasashen Afrika ta yamma mai suna Mista Ketil Karlsen shine ya bayyana hakan a wurin kaddamar da shirin taimakawa Najeriya din.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng