'Yan sara-suka sun kashe Saja, sun tafka ta'asa a gidajen mai uku

'Yan sara-suka sun kashe Saja, sun tafka ta'asa a gidajen mai uku

- Wani dan sanda mai mukamin saja ya rasa ransa yayin da jama'a da dama suka jikkata yayin wani fashi da makami

- Rahotanni sun bayyana cewar Dan sandan, Akor, ya bi 'yan fashin ne da niyyar kama su bayan sun gudu

- Cikin wadanda suka samu rauni har da wani soja da wata budurwa

Wani Saja Akor, ya mutu yayin da yabi wasu 'yan fashi da niyyar kama su yayin da suka zo yin fashi a wasu gidajen man fetur uku dake Igando, a wajen birnin Legas.

Rahotanni sun bayyana cewar 'yan fashin sun harbi saja Akor amma da suka ga harbin bai cinsa sai suka gudu suka bar motar su.

'Yan sara-suka sun kashe Saja, sun tafka ta'asa a gidajen mai uku
'Yan sara-suka sun kashe Saja, sun tafka ta'asa a gidajen mai uku

Akor ya gamu da ajalinsa ne bayan ya bi 'yan fashin da niyyar kama su bayan sun gudu.

KU KARANTA: Jiragen ruwa 29 makare da kayan abinci da man fetur sun fara iso wa Legas a yau

Wani shaidar gani da ido ya shaidawa jaridar The Nation cewar wani soja da wata mata sun samu raunuka sakamakon samun su da harsashi yayi bayan 'yan fashin sun yi harbin iska.

Shaidar ya kara da cewa "dan sandan bashi da wani makami amma duk harbin da 'yan fashin suka yi masa bai yi masa komai ba. Da bakinsa yake fada masu cewar ba zai harbu ba. Ganin haka yasa 'yan fashin suka gudu, shi kuma ya bisu da niyyar kama su."

An samu gawar Saja Akor a wurin tsayawar motoci bayan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng