Yaron Dahiru Bauchi ya kafirta duk wanda yace Shehu Tijjani Allah ne
Daya daga cikin yayan shahararren Malamain addinin Musulunci dake jihar Kaduna, Sheikh Dahiru Bauchi, Sayyed Bashir Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana masu kiran Shehu Tijjani a matsayin Allah, kafirai.
Bashir ya bayyana haka ne a yayin taron Maulidi daya gudana a ranar Lahadi 4 ga watan Feburairu a garin Karshi dake babban birnin tarayya Abuja, inji rahoton Rariya.
KU KARANTA: Tirka tirkan zabukan 2019: Fitattun Sanatoci guda 5 da suka zare da gwamnonin jihohinsu
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Bashir na fadin cewar lokaci yayi da zasu barranta da duk wani dan Darika dake ikirarin Shehu Tijjani ne ubangijinsa, inda yace duk wanda yayi wannan ikirarin ya zama kafiri.
Sayed ya cigaba da fadin don haka jama’a su daina danganta ire iren kafiran nan da darikar Shehu Tijjani. “Idan da ana gudanar da tsarin addinin Musuluci a Najeriya, da hukuncin kisa za’a zartar musu, don kuwa sun fi kafirai kafirci, domin wannan ridda ne, kuma kafiri ba ridda yayi ba.”
Daga karshe Bashir yayi kira ga jama’a da su yi hattara da wadannan mutane, domin a cewarsa, shan giya, zina, da shan taba dukkaninsu haramtattun al’amura ne a darikar Tijjaniyya.
Idan za’a tuna a karshen makon daya gabata ne aka samu hotunan wani mabiyin darikar tijjaniyya a shafukan sadarwar zamani, inda aka gansa dauke da kwalbar giya yana sha, kuma yana daurata a kan Qur’ani.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng