Fursononi 35 sun zana jarabawar WAEC daga gidan yarin jihar Legas
Hukumar kula da gidajen yari, reshen jihar Legas ta ce akalla mazauna gidan Yaris u 35 ne daga kwalejin horar da Fursunoni suna zana jarabawar WAEC da mai suna WASSC na watan Janairu/Feburairu.
Shugaban hukumar na jihar legas, Tunde Oladipo ne ya bayyana haka ga hukumar dillancin labaru, NAN a ranar Lahadi 4 ga watan Feburairu, inda yace suna kokari don ganin sun ilmantar da mazauna gidajen Yari, tare da tabbatar da ingancin walwalarsu.
KU KARANTA: Rikicin addini ya ɓalle tsakanin ɗalibai Musulmai da Kirista a jami’ar Yola
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana fadin “Ina fatan zasu samu kyakkyawan sakamako, duba da irin goyon baya da taimako da muka samu daga kungiyoyi masu zaman kansu, saboda mu sama masu gurbi a budaddiyar jami’ar Najeriya. Yin hakan zai basu damar bada gudunmuwa ga cigaban Najeriya.”
Hakazalika shi ma shugaban makarantar, Idris Ibikunle ya nuna farin cikinsa da wannan cigaba, haka zalika ya yi musu fatan alheri don samun kyakkyawan sakamakon jarabawa.
Daga karshe hukumar ta bukacin taimakon gwamnati don ingantawa tare da habakar kwalejin gidan Yarin da nufin samar da na’urori masu kwakwalwa don fara gudanar da jarabawar JAMB ga mazauna gidajen Yarin.
A wani labarin kuma, batun da ministan al’muran cikin gida, Abdulrahman Dambazau yayi na cewa wai gwamnati na kashe ma kowane Fursuna naira dubu 14 akan abinci a duk rana ya yamutsa hazo, inda jama’a da dama suka musanta maganan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng