Gindin rijiya ba wurin wasan makaho bane - Sanata ya gargadi Matasa masu sha'awar tsayawa takarar siyasa

Gindin rijiya ba wurin wasan makaho bane - Sanata ya gargadi Matasa masu sha'awar tsayawa takarar siyasa

- Tsohon gwamnan jihar Filato kuma Sanata mai wakiltar Filato ta tsakiya, Jonah Jang, ya gargadi matasa masu burin son tsayawa takara da su kiyayi majalisar dattijai

- A wata hira da yayi da manema labarai, Jang, ya ce majalisar dattijai ba ta matasa ba ce

- Kazalika tsohon gwamnan ya yi magana a kan lalacewar dangantaka tsakaninsa da mai ci, Simon Lalong

A wata hira da ya yi da manema labarai, tsohon gwamnan jihar Filato kuma Sanata mai wakiltar Filato ta tsakiya, Jonah Jang, ya gargadi matasa masu burin tsayawa takara da su kiyayi majalisar dattijai.

Yayin hirar da aka gudanar a gidansa dake Du, a Jos ta kudu, Jang, ya bayyana cewar majalisar wakilai ba wurin wargin matasa ba ce.

Gindin rijiya ba wurin wasan makaho bane - Sanata ya gargadi Matasa masu sha'awar tsayawa takarar siyasa
Sanata Jonah Jang

Kazalika, tsohon gwamnan ya bayyana cewar tsofin shugabannin kasa; Babangida da Obasanjo, sun yi daidai a shawarar da suka bawa shugaba Buhari ta ya hakura da batun tsayawa takara a zaben 2019.

DUBA WANNAN: Gwamna Lalong ya yi fashin baki ga hukumar 'yan sanda a kan rigingimun dake faruwa a jihohin arewa ta tsakiya

Jang ya bayyana cewar da iznin Allah shine zai gaji shugaba Buhari a 2019 bayan ya bayyana cewar shugaban kasar ya gaza, kamar yadda jaridar Legit.ngta sanar maku a daya daga cikin labaranta.

Da yake magana a kan lalacewar dangantaka tsakaninsa da gwamnan jihar, Simon Lalong, Jang, ya ce tun bayan rantsar da gwamnan basu kara haduwa ba duk da ya taba rubuta takardar gayyata ga gwamnan domin tattaunawa ta musamman.

Jang ya zargi gwamna Lalong da rashin bashi girma domin, a cewar sa, ko a shekarun haihuwa gaba yake da gwamnan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng