Tirka tirkan zabukan 2019: Fitattun Sanatoci guda 5 da suka zare da gwamnonin jihohinsu
Tun bayan lallasa jam’iyyar PDP a zabukan gamagari na 2019 ne dai Jam’iyyar APC ta shiga halin rikice rikice na cikin gida, wanda ya sa ta zamo tamkar matar nan da ake yi ma kirari da suna ‘Iya rigima’.
Da dama, rikita rikitan na faruwa ne tsakanin gwamnonin jihohin da APC ke mulki da kuma Sanatocin jam’iyyar dake wakiltar al’ummun jihar a majalisar dattawan Najeriya, sau dayawa Sanatocin suna ganin gwamnan bai isa dasu bane, don haka ba zasu ba shi kai bori yah au ba.
KU KARANTA: Tsugunni bata ƙare ba: Matasan ƙabilar Tibi sun sake kai ma Hausawa hari a Benuwe
Legit.ng ta binciko wasu sanannun Sanatocin Najeriya da basa ga maciji da gwamnonin jihohinsu, daga cikinsu akwai:
Sanata Shehu Sani (Kaduna ta tsakiya) da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Sanata Dino Melaye (Kogi ta yamma) da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso (Kano ta tsakiya) da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje
Sanata Kabiru Marafa (Zamfara ta tsakiya) da gwamnan jihar Abdul Azizi Yari
Sanata Abu Ibrahim (Katsina ta kudu) da gwamnan jihar Aminu Bello Masari
Sai dai tambayar da jama’a da dama ke yi itace, shin Sanatocin nan da suka riga suka nuna maitarsu a fili game da bukatar komawa kujerarsu zasu iya kai bantensu kuwa?, musamman yadda ake ganin gwamnoni ke juya akalar jam’iyya a jihohinsu.
Lokaci ne kadai ka iya tabbatar da wannan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng