Majalissar wakillai ta bayyana ainihin kudaden da suka bace a hukumar NIA

Majalissar wakillai ta bayyana ainihin kudaden da suka bace a hukumar NIA

- Majalissar wakillai ta ce dala miliyan $404m suka bace a hukumar NIA

- Wasu daraektocin hukumar NIA sun bukaci majalissar wakillai ta sauke Ahmed Rufai daga mukamin shugaban hukumar NIA

Kwamitin majalissar wakilai dake kula da al’amuran jami’an tsaro ta ce dala miliyan $404m ne ainihin adadin kudaden da suka bace a hukuma lekan asiri (NIA) sabanin rahotannin farko da suka nuna dala miliyan $44m kacal suka bace.

Shugaban kwamitin, Mista Aminu Sani-Jaji, ya ce $44m basu bace ba an kai su wani wurin ajiya ne.

Amma, Sani Jaji ya ce dala miliyan $202 sun bace a hukumar NIA kuma ba a san inda suke ba.

Majalissar wakillai ta bayyana ainihin kudaden da suka bace a hukumar NIA
Majalissar wakillai ta bayyana ainihin kudaden da suka bace a hukumar NIA

Kwamitin ta na binciken matsalolin dake kewaye da nada Ahmed Rufai, a matsayin babban daraektan hukumar NIA da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi.

KU KARANTA : Gwamnonin jam'iyyar PDP 11 sun yi ganawar sirri a garin Asaba

Rahotanni sun nuna cewa Ahmed Rufai ya taba faduwa jarabawa karin girma har sau biyu, bayan haka ana zargin, Ahemd Rufai, da kansancewa dan kasar Chadi ne ba dan Najeriya ba.

Wannan dalili yasa majalissar wakillai ta umarci kwamitin, Sani Jaji ta bincike al’amarin yayin da wasu daraektocin hukumar NIA suka bukaci majalissar ta sauke, Rufai Abubakar, daga mukamin babban daraektan hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng