Gwamnatin Iraqi na neman 'yar Marigayi Saddam da wasu mutane 59 ruwa a jallo

Gwamnatin Iraqi na neman 'yar Marigayi Saddam da wasu mutane 59 ruwa a jallo

- Gwamnatin kasar Iraqi na neman babban dan tsohon shugaban kasa, Marigayi Saddam Hussein, da ragowar wasu mutane 59

- Hukumomin kasar na nemansu ne bisa zargin suna da hannu a kungiyar al-Qaeda ko jam'iyyar al-Baath

- 'Yar marigayi Saddam, Raghad, ta yi gudun hijira ya zuwa kasar Jordan tun shekarar 2003

Hukumomin tsaro a kasar Iraqi sun bayyana babbar 'yar tsohon shugaban kasar, Marigayi Saddam, Raghad, da wasu mutane 59 a matsayin wadanda suke nema ruwa a jallo.

Hukumomin na neman mutanen ne bisa zarginsu da kasancewa mambobin kungiyar al-Qaeda ko jam'iyyar al-Baath.

Gwamnatin Iraqi na neman 'yar Marigayi Saddam da wasu mutane 59 ruwa a jallo
Marigayi Saddam Hussein

Saidai babbar 'yar Saddam din, Raghad, ta shaidawa gidan talabijin din Al Arabiya, na kasar Saudiyya, ta wayar tarho cewar za ta shigar da karar gwamnatin kasar bisa zargin ci mata mutunci.

DUBA WANNAN: Mai duba lafiyar matar Shekau ta saduda, ta mika wuya ga jami'an tsaro

Raghad da 'ya'yanta sun tsere ya zuwa kasar Jordan inda take zaune tun watan Yuli na shekarar 2003 kuma ta kasance cikin jerin wadanda hukuma ke nema tun shekarar 2016 bisa zarginta da goyon bayan aiyukan ta'addanci.

Saidai kasar Jordan ta ki amincewa da bukatar kasar Iraqi na mika mata Raghad, tana mai bayyana cewar yin hakan ya saba da al'adar Larabawa ta nuna karamci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng