Tsugunni bata ƙare ba: Matasan ƙabilar Tibi sun sake kai ma Hausawa hari a Benuwe
Har zuwa yanzu tsuguni bata kare ba a jihar Benwue, tun bayan da rikici tsakanin Fulani da makiyaya ya barke a jihar, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan jama’a.
A nan ma an sake kwatawa ne, inda Rariya ta ruwaito cewa matasan kabilar Tibi dake jihar Benuwe sun kar ma wasu Hausawa hari yayin da suke tafiya a cikin motarsu, tare da farfasa Motar.
KU KARANTA: Waiwaye adon tafiya: Gwamna Ganduje ya tuna lokacin da yake kiwon shanu (Hotuna)
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Feburairu a garin Wanune dake cikin karamar hukumar Tarka na jihar Benuwe.
Idan za’a tuna ko a satin daya gabata sai da matasan kabilar Tibi suka hallaka wasu mutanen kabilar Hausa Fulani su hudu yayin da suka shiga wani tashar mota da nufin tafiya, inda matasan suka babbaka gawarsu.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya yayi kamari a jihar Benuwe tun bayan kaddamar da dokar hana kiwo da gwamnatin jihar ta kirkiro da nufin kauce ma rikicin, amma hakan bai haifar da da mai ido ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng