Tsaro: Rundunar Sojin Najeriya za ta kafa bariki a garin Jalingo, jihar Taraba
- Rundunar Sojin Najeriya za ta kafa bariki a garin Jalingo, jihar Taraba
- Sun ce su kammala dukkan shire-shiren da suka wajaba wajen tabbatar da gina sabon barikin sojojin
- Babban hafsan sojojin na bataliya ta 3 dake a garin Jos Manjo Janar Benjamin Ahanotu ne ya bayyana hakan
Rundunar sojin kasan Najeriya ta sanar da kammala dukkan shire-shiren da suka wajaba wajen tabbatar da gina sabon barikin sojoji a garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba domin tabbatar da tsaro.
Babban hafsan sojojin na bataliya ta 3 dake a garin Jos Manjo Janar Benjamin Ahanotu ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar bangirma da ya kaiwa gwamnan jihar ta Taraba Mista Darius Ishaku a ofishin sa.
KU KARANTA: Hanyoyin sadarwa na gargajiya a kasar Hausa
Legit.ng ta samu dai cewa Manjo Janar Benjamin ya bayyana cewa musabbabin makasudin zuwan na sa bai rasa nasaba da kammalar shire-shiren su na kafa barikin.
A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa akalla gwamnonin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP a takaice ne suka yi wani taron ganawa na bayan labule da kwamitin gudanarwar jam'iyyar watau National Working Committee, NWC a takaice a garin Asaba na jihar Delta.
Gwamnonin da suka halarci taron dai sun hada da Alhaji Hassan Damkwambo (Gombe), David Umahi (Ebonyi), Siareke Dickson (Bayelsa), Udom Emmanuel (Akwa-Ibom), Nyesom Wike (Rivers).
Sauran sun hada da Ayodele Fayose (Ekiti), Okezie Ikpazu (Abia), Darius Ishaku (Taraba), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Ben Ayade (Cross Rivers) sai kuma mai masaukin baki , Ifeanyi Okowa (Delta).
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng