Gobe Buhari zai kai ziyarar aiki ta wuni 1 zuwa jihar Nasarawa

Gobe Buhari zai kai ziyarar aiki ta wuni 1 zuwa jihar Nasarawa

- Gobe Buhari zai kai ziyarar aiki ta wuni 1 zuwa jihar Nasarawa

- Mun samu dai cewa a yayin ziyarar ta sa, shugaban zai kaddamar da makarantar masu larura ta musamman dake garin Lafiya

- Gwamnan jihar Alhaji Tanko Almakura ya bayyana cewa tuni jihar ta kammala shire-shiren zuwan

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa gobe shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai shilla zuwa wata ziyarar wuni daya a garin lafiya, jihar Nasarawa dake makwaftaka da garin Abuja.

Gobe Buhari zai kai ziyarar aiki ta wuni 1 zuwa jihar Nasarawa
Gobe Buhari zai kai ziyarar aiki ta wuni 1 zuwa jihar Nasarawa

KU KARANTA: Jam'iyya ta bulla da zata takawa PDP da APC burki a 2019

Mun samu dai cewa a yayin ziyarar ta sa, shugaban zai kaddamar da makarantar masu larura ta musamman dake garin Lafiya, sai kuma kasuwar kasa-da-kasa dake garin Karu da kuma tashar samar da wutar Lantarki mai karfin 330KVA.

Legit.ng ta samu kuma haka zalika cewa gwamnan jihar Alhaji Tanko Almakura ya bayyana cewa tuni jihar ta kammala shire-shiren zuwan shugaban kasar a jihar ta sau.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa akalla gwamnonin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP a takaice ne suka yi wani taron ganawa na bayan labule da kwamitin gudanarwar jam'iyyar watau National Working Committee, NWC a takaice a garin Asaba na jihar Delta.

Gwamnonin da suka halarci taron dai sun hada da Alhaji Hassan Damkwambo (Gombe), David Umahi (Ebonyi), Siareke Dickson (Bayelsa), Udom Emmanuel (Akwa-Ibom), Nyesom Wike (Rivers).

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng