Waiwaye adon tafiya: Gwamna Ganduje ya tuna lokacin da yake kiwon shanu (Hotuna)
A ranar Lahadi, 4 ga watan Feburairu ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci ayarin shuwagabannin gwamnatin jihar Kano don kaddamar da aikin alluran shanu a jihar.
Wannan bikin kaddamar da alluar shanu ya gudana ne a garin Kadawa na jihar Kano, inda aka hangi gwamnan yana sanye da kayan Fulani daga sama har kasa, tare da rike sandan kiwo nay an Fulani, mai suna Laggel.
KU KARANTA: Jerin muhimman kalmomin hausa 20 da ma'anar su a harshen turanci
Hakazalika mai gayya mai aiki, Kwamishinan harkar noma na jihar, Abdullahi Gawuna an hange shi sanye da kayan Fulani shi ma, inda a yayin taron gwamnan jihar Kano ya fara tsira ma wani shanu allura.
Legit.ng ta ruwaito a yayin taron gwamnan ya kaddamar da kayayyakin aikin allurer rigakafin, wadanda ya mika su ga jami’an gudanar da alluran a kauyen Kadawa, inda yace ya san da wuya a samu Fulani dan asalin jihar Kano, amma yana kira da su dawo jihar Kano da dabbobinsu don gudun rikici da manoma.
Daga karshe Gwamnan yace gwamnatinsa ta tura makiyaya guda 60 zuwa kasashen Turai don samun horo game da tsarin kiwon dabbobi na zamani, tare da iya amfani da na’urorin dake amfani dasu wajen kiwon.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya mika ma makiyaya goron gayyata da su kado dabbobinsu zuwa jihar Kano don ci gajiyar labobin kiwo da jihar ta mallaka a kananan hukumomin Ungogo, Kura, Garun Malam da sauransu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng