Menene gaskiyar rahotanni da ke yawo cewa wai Sarauniyar Ingila na kalen dangi da annabi

Menene gaskiyar rahotanni da ke yawo cewa wai Sarauniyar Ingila na kalen dangi da annabi

- Ana ta yamadidi da zancen wai Sarauniyar Ingila ta ce ita jinin annabi ce a kasashen musulmi

- Wannan zance dai bashi da makama balle tushe, sai soki burutsu

- Zubar da aji ne mutane su yada karya domin kawai son ransu

Menene gaskiyar rahotanni da ke yawo cewa wai Sarauniyar Ingila na kalen dangi da annabi
Menene gaskiyar rahotanni da ke yawo cewa wai Sarauniyar Ingila na kalen dangi da annabi

A makonnin nan, a kasashen musulmi, ana ta yamadidin cewa wai ai sarauniyar Ingila ta ce ita sharifiya ce jikar annabi, inda har mutane kan yada hotunan ta da lullubi ko ta rike Qur'ani.

Wannan labari dai kanzon-kurege ne, abin da a turance ake kira fake news. Bashi da tushe balle makama, Sarauniyar bata ma san ana yi ba, BBC da ake cewa tayi rahoton ba gaskiya bane. Hasali ma, sarauniyar ta Ingila baturiya ce ba balarabiya ba.

A tarihin masaratar Ingila, da ta Windsor gidan sarautar, an san cewa asalin tsatson su ya fito ne daga kasar Jamus, sannan ana iya bin diddigin iyaye da kakanni na masarautar, babu wani jini na larabci a gidansu.

A kimiyyance dai, ko kai ma da ita sarauniyar, da ma Makel Jackson, da Dangote, Annabin, da Ali Makaho, duk kakannin mu daya, amma babu wata dangantaka ta layi tsakanin annabi da baturiyar Ingila.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya sake shan suka daga Janar Babangida

Hotunan da suke yada wa kuwa, sukan dauko ne daga ziyarar ta a kasashen larabawa da ma kasar Turkiyya, da ziyarar da tayi a baya ta masallatai.

Sai kuma inda ta gana da limamai ko aka bata kyautar Qur'ani, sai su dauki hoton, su yada, domin kalen dangi da zubdawa da kai aji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng