Janar Babangida ya kira shugaba Buhari ya bar wa yara a 2019

Janar Babangida ya kira shugaba Buhari ya bar wa yara a 2019

- Watakil shugaba Buhari na neman tazarce ne

- Manyan kasa na gani ya tsuffa da yawa yace zai zarce

- A yanzu dai Obasanjo na jan ragamar taron dangi kan yakar Buhari

Janar Babangida ya kira shugaba Buhari ya bar wa yara a 2019
Janar Babangida ya kira shugaba Buhari ya bar wa yara a 2019

Janar mai ritaya, Ibrahim Badamasi Babangida, yayi kira ga 'yan Najeriya dacsu zabi samari su mulke su a 2019, domin samun ci-gaban kasa da sabon jini a Aso Rock.

Ya kuma shawarci kaninsa Janar Muhammadu Buhari, da ya hakura da mulki yayi ritaya a 2019 ya koma Daura, domin ya fuskanci batun lafiyarsa. Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su baiwa Buharin hadin kai domin ya karasa aikinsa na shekara hudu.

An dai ga ministocin Buharin suna yada fastarsa ta tazarce a 2019 martani ga Obasanjo da ya kira shugaban da ya ajje mulki a badi.

DUBA WANNAN: Fashola yace matsalar lantarkin Najeriya ba ta yau bace

Janar BAbangida dai, ya nemi mulki a 2007, amma ya ajje takararsa, bayan da Obasanjo yace ba Babangidan za'ayi ba, a PDP, Ummaru 'Yar'aduwa zai mika wa mulki.

Ga alama dai, manyan kasar nan na so Buhari ya barwa masu karancin shekaru su ggwada irin nasu salon ne, su kuwa dattijan, su koma su huta a ritaya.

Ba'a sa rai Buharin ko gwamnatinsa zasu ji wannan kira na Janar Babangida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng