Zaben 2019 : Obasanjo da Kwankwaso ba za su iya takawa Buhari birki ba – Hadimin shugaban kasa
- Kawu Sumaila ya ce Kwankwaso da Obasanjo ba za su iya hana Buhari dawowa kan kujerar shugaban kasa a zaben 2019 ba
- Kawu Sumaila ya ce Obasanjo bai isa ya fadawa 'yan Najeriya dan takarar da za su zaba ba
Mai ba wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawara akan al’amuran da ya shafi majalissar wakillai, Alhaji Suleiman Abdurahaman wanda aka fi sani da Kawu Sumaila, ya ce hadakar kungiyar, Cif Olusegun Obasanjo, da na Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba za su iya hana Buhari dawowa kan kujerar shugaban kasa a zaben 2019 ba.
Da yake jawabi a lokacin da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinabjo, ya ziyarci jihar Kano dan halarta bikin daurin auren wani hadimin sa, Alhaji Kawu, ya ce tsohon shugaban kasa, Obasanjo, bashi da izinin da fadawa ‘yan Najeriya wanda za su zaba a 2019.
“Idan ‘yan Najeriya sun amince Buhari yakara tsayawa takara, Obasanjo bashi da wata zabi illa ya bar su su zabi wanda suke so.
KU KARANTA : Gwamnatin Jihar Katsina za ta dauki Malaman asibiti aiki
Ya tabbatar da cewa, budadiyar wasikar da Obasanjo ya aika wa Buhari ba zai karkatar da hankalin shugaban kasa daga cigaba da kyawawan ayyuka da ya fara yiwa kasar ba.
“Mun shirya wa Obasanjo, Kwankwaso da duk wani wanda yake so ya kawo wa siyasar mu cikas”, inji Sumaila.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng