Daruruwan mutane na kaura daga gidajensu a jihar Taraba

Daruruwan mutane na kaura daga gidajensu a jihar Taraba

- Daruruwan mutane na cigaba da tserewa daga gidajensu a garuruwan Gassol, Ibi, da Wukari a jihar Taraba

- Jama'ar na kauracewa gidajensu ne saboda tsoron harin fansa da makiyaya kan iya kawowa kan mazauna garuruwan

- Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ne ya fara kwarmata cewar makiyaya na shirin kai hare-haren daukan fansa a kananan hukumomin

Daruruwan mutane na cigaba da kauracewa gidajensu a wasu garuruwan kananan hukumomin Gassol, Ibi, da Wukari a jihar Taraba saboda tsoron harin fansa da makiyaya kan iya kaiwa kan mazauna garuruwan.

A ranar Laraba da ta gabata ne gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya kwarmata cewar makiyaya na shirin kai harin daukan fansa a kan al'ummar yankin.

Daruruwan mutane na kaura daga gidajensu a jihar Taraba
Daruruwan mutane na kaura daga gidajensu a jihar Taraba

Jaridar Punch ta rawaito cewar an kashe mutane biyar a garin Jembe dake karamar hukumar Wukari da kuma wasu mutane hudu a kauyen Ngutswen a karamar hukumar Gassol, sa'o'i tara bayan gwamnan ya yi ikirarin.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa rikicin makiyaya da manoma har yanzu bai kare ba - Gwamna Yari

Jaridar Punch ta wallafa rahoton cewar mutanen kauyukan na cigaba da kauracewa gidajensu saboda makiyaya sun ci alwashin daukan fansar kisan 'yan uwansu a kan 'yan kabilar Tiv.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, David Missal, ya shaidawa jaridar Punch ta wayar tarho cewar duk da kasancewar basu tura karin jami'ansu yankin ba bayan ikirarin da gwamnan ya yi, jami'an hukumar na cikin shirin ko-ta-kwana.

A baya Legit.ng ta kawo maku rahotonni akan rikici tsakanin makiyaya da manoma dake cigaba da lakume rayuka a wasu jihohin arewa ta tsakiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng