Cin kofin Afrika: Nigeria za ta cakusa da kasar Morocco a wasan karshe

Cin kofin Afrika: Nigeria za ta cakusa da kasar Morocco a wasan karshe

- Nigeria za ta cakusa da kasar Morocco a wasan karshe

- Kasar ta Nigeria dai ta samu nasarar cin kasar Sudan 1-0 a wasan daf da karshe da aka buga a ranar Laraba

- Yanzu dai za'a doka wasan karshe ne tsakanin Morocco da Nigeria a ranar Lahadi

Kawo yanzu dai kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya watau Super Eagles ta samu nasarar kaiwa wasan karshe a cigaba da ake yi da gasar cin kofin nahiyar Afirka ta yan wasan da ke murza leda a nahiyar da ake kira CHAN.

Cin kofin Afrika: Nigeria za ta cakusa da kasar Morocco a wasan karshe
Cin kofin Afrika: Nigeria za ta cakusa da kasar Morocco a wasan karshe

KU KARANTA: Kayatattun kalar rawar gargajiyar Hausa 4

Kasar ta Nigeria dai ta samu nasarar cin kasar Sudan 1-0 a wasan daf da karshe da aka buga a ranar Laraba da ta gabata.

Legit.ng ta samu cewa a wasan kungiyar ta Najeriya ta Super Eagles ta zura kwallon ta ne ta hannun Gabriel Okechukwu a minti na 16 da fara tamaula.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kasar ta Nigeria ta kammala buga wasan da yan wasa 10 bayan da aka bai wa Ifeanyi Samuel Nweke jan kati, kamar dai yadda ita ma Sudan din aka korar mata dan wasa Bakri Basheer.

Ita kuwa Morocco nasarar cin Libya 3-1 ta yi.

Yanzu dai za'a doka wasan karshe ne tsakanin Morocco da Nigeria a ranar Lahadi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng