Rundunar sojin sama ta kasa ta yaye dalibai 5,707 cikin kasa da shekaru 3

Rundunar sojin sama ta kasa ta yaye dalibai 5,707 cikin kasa da shekaru 3

- Rundunar sojin sama ta kasa ta yaye dalibai 5,707 cikin kasa da shekaru 3

- A jiya an yaye wasu daliban ta guda 1,544 da suka kammala daukar horo a makarantar koyon aikin sojin

- Hafsan sojin saman Najeriya Cif Sadique Abubakar ya bayyana haka

Rundunar sojin saman Najeriya watau Nigerian Air Force (NAF) a turance a jiya ta yaye wasu daliban ta guda 1,544 da suka kammala daukar horo a makarantar koyon aikin sojin sama dake a garin Kaduna.

Da yake jawabi yayin bukin yaye daliban, hafsan sojin saman Najeriya Cif Sadique Abubakar ya bayyana cewa kawo yanzu a cikin kasa da shekaru uku rundunar ta yaye dalibai akalla 5,707 tun bayan hawan sa kan kujerar sa.

Rundunar sojin sama ta kasa ta yaye dalibai 5,707 cikin kasa da shekaru 3
Rundunar sojin sama ta kasa ta yaye dalibai 5,707 cikin kasa da shekaru 3

KU KARANTA: Dalilin da ya sa yaran Najeriya ba su son lissafi

Legit.ng ta samu cewa ya bayyana hakan a matsayin wani mataki da suke dauka wajen ganin an ida kakkabe dukkan birbishin rashin zaman lafiya da kasar ke fama da shi.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a cikin makon jiya ne ma dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da shugabannin jami'an tsaron kasar da nufin kawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi a jihohin kasar nan.

A wani labarin kuma, Jami'an rundunar sojin saman Najeriya sun samu nasarar yiwa 'yan ta'addan nan na Boko Haram da yanzu haka suke gudun hijira a dajin Sambisa a jihar Borno luguden wuta ta sama inda suka samu nasarar lalata wata babbar motar harba makamai ta kungiyar.

Jami'an hulda da jama'a na rundunar da kuma harkokin yada labarai watai Air Vice Marshal Olatokunbo Adesanya shine ya sanar da hakan ga manema labarai a jiya Alhamis, 1 ga watan Fabrairun shekara ta 2018.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng