Tsaro: Zamu watsa dakaru cikin yankuna daban-daban - Buratai
Shugaban hafsin sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana cewa, a kwana-kwanan nan za su ƙaddamar da sabbin atisaye, inda zasu watsa dakaru yankuna daban-daban na ƙasar domin fuskantar ƙalubalen tsaro dake ci gaba da ta'azzara a faɗin ta.
Yake cewa, za a watsa dakarun ne wasu sassan ƙasar nan da suka haɗar da yankunan kudu maso gabas, yankin Neja Delta, yankin kudu maso yamma da kuma yankin Arewa inda za shawo kan matsalar sace-sace shanu da rikicin makiyaya.
Da wannan ne yake kiran dakaru a kan su kasance cikin shiri, domin a kowane lokaci ana iya watsa su domin sauke nauyin da rataya a wuyansu na bai wa ƙasar nan tsaro da kuma kariya.
Shugaban sojin ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, a yayin da yake jagorantar wasu dakaru wajen gudanar da atisaye tare da motsa jiki a barikin soji na Mogadishu dake babban birnin ƙasar nan.
A yayin da za a gudanar da atisaye a yankin kudu, shugaban soji ya bayyana cewa, hakan zai tabbatu ne domin daƙile matsalolin fashe bututun man fetur da satar sa, tayar da ƙayar baya da kuma garkuwa da mutane.
KARANTA KUMA: Kujerun gwamnoni 5 da sai an kai ruwa rana a zaben 2019
Sai dai jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Buratai bai bayar da tabbaci ba na watsa dakaru jihohin Binuwai, Taraba da kuma Nasarawa a sakamakon gwagwarmaya tsakanin makiyaya da manoma da ta yi sanadiyar salwantar rayukan al'umma da dama.
A yayin haka kuma, Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai jerin gwamnoni biyar da zasu tafka baƙin gumurzu a jihohin su domin samun nasarar lashe zaɓen 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng