Majalisar dokoki ta rattaba hannu a kan sabbin dokoki 9 a jihar Jigawa

Majalisar dokoki ta rattaba hannu a kan sabbin dokoki 9 a jihar Jigawa

Majalisar dokoki ta jihar Jigawa, ta zartar da amincin ta kan wasu sabbin dokoki 9 cikin 15 da kundin tsarin kasa ya tanadar, ciki har da sabuwar dokar nan da take bai wa matasa damar takarar siyasa wanda majalisar zartaswa ta gindaya a sauyin kundin na kasa.

Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Badaru Abubakar
Gwamnan jihar Jigawa; Muhammad Badaru Abubakar

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, akwai wasu dokoki da majalisar dokokin ba ta aminta da su ba wadanda suka hadar da dokar yiwa umarnin shugaban kasa haye da kutsu, wa'adi akan lokacin shigar da kasafin kudi tare da shinfida ta kididdigar babban jigo na kasafin kudi.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta sake kwaso 'yan Najeriya 465 daga ƙasar Libya

Legit.ng ta fahimci cewa tun watan Dasumbar shekarar 2016 ne, majalisar zartaswa ta kafa kwamitin nazari domin sauya wasu muhimman sashe a cikin kundin tsarin kasa na 1999.

A sakamakon haka ne, majalisar zartaswa ta bayar da lamuni akan sauya wasu muhimman dokoki 15, inda ta nemi amincewar majalisun dokoki na jihohin kasar nan tun a ranar 14 ga watan Dasumbar shekarar da ta gabata.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta sake kwaso 'yan Najeriya 465 daga kasar Libya, inda ta yasar da su a filin jirgin sama na birnin Fatakwal a ranar Juma'a ta yau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng