Da dumi-dumi: Yan Boko Haram 26 sun mika wuya
Yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram ashirin da shida sun saduda sun mika wuya ga jami’an soji karamar hukumar Damboa, jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya.
An bayyana yan ta’addan da suka tuba a ranan Juma’a a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan bincike da aka gudanar a kansu.
Rahoto ya nuna cewa sun mika wuya makon da ya gabata ne kuma sun sallamar da dukkan makamansu sannan aka kaisu garin Maiduguri domin gyaran tunani.
KU KARANTA: Ku fifita cancanta fiye da komai a yayin zaben shuwagabanni - Buhari ga matasan Najeriya
Zaku tuna cewa jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa dakarun sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram a dajin Sambisa har sun fara gina hanya a cikin dajin don tabbatar wa duniya cewa lallai a cin galaban yan Boko Haram.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng