Gwamnatin tarayya ta sake kwaso 'yan Najeriya 465 daga ƙasar Libya
A cikin shirin gwamnatin tarayya da take ci gaba da aiwatar wa na yaso 'yan asalin ƙasar Najeriya daga ƙasar Libya, ta sake ciccibo wani ayari da suka shiga ƙangin ƙaƙani-kayi, inda suka sauka a filin jirgin sama na Fatakawal da misalin ƙarfe 12:25 na yau Juma'a.
Wannan ayari na 'yan Najeriya 465 sun sharo sararin samaniya ne a cikin jirgi na kamfanin Max Air, inda ma'aikata na cibiyar bayar da agaji na gaggawa da sauran cibiyoyi masu ruwa da tsaki suka tarbe su.
Legit.ng da sanadin channels TV ta fahimci cewa, gwamnatin tarayya ta na ci gaba da yaso 'yan Najeriya tun watannin da suka gabata, musamman bayan da rahoton cinikayyar bayi ya tashi hankali duniya, inda ake wulakanta al'umma nahiyyar Afirka a yayin da suke yunkurin ketare wa zuwa kasashen turai.
KARANTA KUMA: Wasiƙar Obasanjo: Ko kadan bana baƙin ciki da shugaba Buhari - Obasanjo
Rahotanni sun bayyana cewa, akan cafke bakin hauren ne a yayin da suke ƙoƙarin ƙetare tekun bahar Maliya zuwa ƙasashen Turai, wanda bincike ya tabbatar da cewa, akwai baƙin haure da suka samu nasarar haurewa zuwa kasar Italiya tun daga shekarar 2014, inda kimanin 12,000 suka rasa rayukan su a yayin yunkurin hakan.
A yayin da masu fada a ji na kasar nan suka nemi a kawo ƙarshen wannan cuzguni, gwamnatin tarayya a na ta bangaren ta ce za ta yi iya ka bakin ƙoƙarin ta wajen maido da 'yan Najeriya gida.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Obasanjo ya sake caccakar gwamnatin shugaba Buhari dangane da yadda ya yi watsi da cigaban kasa wajen rarraba muƙaman gwamnati.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng