Rikicin jihar Benuwe: Attahiru Bafarawa ya kai ziyarar jaje, ya raba ma yan gudun hijira naira miliyan 10

Rikicin jihar Benuwe: Attahiru Bafarawa ya kai ziyarar jaje, ya raba ma yan gudun hijira naira miliyan 10

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Dalhatu Bafarawa ya kai ziyarar jajantawa ga gwamnatin jihar Benuwe tare da ilahirin jama’anta sanadiyyar rikicin Fulani da manoma da ya lakume rayuka da dama.

Rariya ta ruwaito da safiyar ranar Juma’a 2 ga watan Feburairu ne jirgin tsohon gwamnan ya sauka a filin sauka da tashin jirage dake garin Makurdi na jihar Benuwe, daga nan kuma tare da yan rakiya suka dunguma sai fadar gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Ku fifita cancanta fiye da komai a yayin zaben shuwagabanni - Buhari ga matasan Najeriya

Rikicin jihar Benuwe: Attahiru Bafarawa ya kai ziyarar jaje, ya raba ma yan gudun hijira naira miliyan 10
Tare da Gwamnan

A yayin ziyarar, Bafarawa ya bayyana alhininsa game da asarar rayuka da dukiyoyi da aka tafka a sakamakon rikice rikicen, kuma yayi fatan Allah ya kiyaye gaba, tare dawwamar zaman lafiya a jihar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bayan mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar tare da mukarrabansa, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya mika kyautan naira miliyan goma ga iyalan wadanda suka mutu daga bangarorin Tibi da na Fulani.

Rikicin jihar Benuwe: Attahiru Bafarawa ya kai ziyarar jaje, ya raba ma yan gudun hijira naira miliyan 10
Attahiru Bafarawa

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom ya sanar da karin tukuici mai tsoka zuwa N50m ga duk wanda ya bada sahihin bayani dangane da wani kasurgumin dan bindiga daya addabi jihar mai suna Gana.

Rikicin jihar Benuwe: Attahiru Bafarawa ya kai ziyarar jaje, ya raba ma yan gudun hijira naira miliyan 10
Tare da gwamnan

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng