Kasashen Larai na kokarin kawo karshen yakin Yemen, kasashen Turai na goyon bayan shirin

Kasashen Larai na kokarin kawo karshen yakin Yemen, kasashen Turai na goyon bayan shirin

- Fadan Larabawa yaki ci yaki cinyewa kusan shekaru 8

- Yemen ta ruguje tun bayan juyin juya hali daya kifar da gwamnatin Abdalla Saleh

- Saudiyya da Iran na kokarin karbe iko da kasar

Kasashen Larai na kokarin kawo karshen yakin Yemen, kasashen Turai na goyon bayan shirin
Kasashen Larai na kokarin kawo karshen yakin Yemen, kasashen Turai na goyon bayan shirin

Tun 2011, juyin juya hali ya hadiye kasashen larabawa, sai dai wsu kasashen sun ruguje gabaki daya, musamman kasar Yemen, wadda ta rushe sakamakon kokarin yan tawayen Houthi wadanda Iran ke mara wa baya da suka kwace mulki.

Kasar Saudiya dai mai bin sunna ta yi ta kai hari kan kasar ta Yemen, inda aka ci gaba da yaki wanda har yayi sanadiyar kisan tsohon shugaba Abdalla Saleh a bara.

A yanzu dai kasashen UAE mai Dubai, da Saudiyya, na kokarin hada kai domin hado kan masu tada kayar baya na kungiyoyin Sunni daban daban domin su samu su kawar da gwamnatin Houthi mai mulki.

DUBA WANNAN: An hana kwastam shiga kasuwanni kame

Kasashen Turai dai sun mara wa shirin baya, wanda zai game kungiyoyin da kasashe daban daban ke baiwa kudi da goyon baya domin a kawo karshen fadan.

A Yemen dai, ana yunwa da cutar kwalara, wadda yakin ne musabbabinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng