Makami mai linzamin da Amurka ta gwada domin kalubalantar Koriya ta Arewa bai yi nasara ba
- Makami mai linzamin da Amurka ta gwada a yankin Hawai bai yi nasara ba
- A farkon wannan shekara shugaban kasar Koriya ta Arewa ya ce makunnin nukiliyya yana kan teburin sa kuma za ba da umarin amfani da shi inda kasar sa ta fuskanci barazana
An bayyana cewa makamai mai linzami da kasar Amurka ta gwada domin kalubalantar kasar Koriyta ta Arewa bai yi nasara ba.
Amurka ta harba makami mai linzamin Aegis Ashore daga jirgin yakin ruwa wanda ya tuntsure ya fado kasa bayan an harba shi.
Hukumar ma’aikatan jami’an tsaron kasar Amurka ta gwada makami mai linzamin Aegis Ashore a yankin Hawaii.
Kamar yadda gidan talebijin din CNN ta bayyana dangane ga nazarin masanan kimiya makamin da kamfanin Rheython ta kera ba za'a iya harbashi daga jirgin sama ba.
KU KARANTA : Matakai 6 da Shugaba Buhari ya dauka domin warware rikicin Binuwai
Amurka ta kera makamin ne don kalubalantar makaman linzaman da kasar Koriya ta Arewa ke amfani da su
A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito muku labarin Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jon Un, inda yace shi fa yana da makunnin nukilliya akan teburin sa, kuma zai ba da umarnin amfani da makaman ne in har kasar sa ta fuskanci barazana daga kasar Amurka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng