Yan sanda sun saka kazar karfi ga duk wanda ya bada sirrin makasan dan siyasar Kaduna
- Yan sanda sun saka kazar karfi ga duk wanda ya bada sirrin makasan dan siyasar Kaduna
- An dai harbe babban dan siyasa Mista Moses Banka daga karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna a wani kauye da ake cema Ankwa
- Shugaban karamar hukumar ta Jema'a Alhaji Yusuf Usman ya tabbatar da faruwar lamarin
Labarin da ke iske mu yanzu da dumin sa na nuni ne da cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun harbe wani babban dan siyasa Mista Moses Banka daga karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna a wani kauye da ake cema Ankwa na karamar hukumar Jema'a duk dai a jihar ta Kaduna.
KU KARANTA: APC a jihar Kano ta ajiye tsintsiya ta dauke makami - PDP
Majiyar mu dai ta tabbatar mana da cewa shugaban karamar hukumar ta Jema'a Alhaji Yusuf Usman ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya bayyana cewa an kashe shi ne a ranar larabar da ta wuce a gidan sa.
Legit.ng dai ta samu cewa maharan da ake kyautata zaton daukar hayar su aka yi sun shiga gidan sa ne da tsakar dare inda suka nufi dakin sa suka kuma harbe shi sannan suka fita ba tare da sun taba kowa ba.
To sai dai tuni jami'an yan sandan jihar a ta bakin jami'in hulda da jama'a ya bayyana cewa rundunar ta saka lada mai yawan gaske ga dukkan wanda ya bayyana wasu bayanan da suka taimaka har aka kama maharan.
A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar dake adawa a jihar Kano a yankin arewa maso yammacin Najeriya wato PDP, ta zargi jam'iyya mai mulki ta ApC a jihar da watsar da tsintsiya da kuma daukar makami.
Jam'iyyar ta PDP din dai ta ce, APC da dukkanin daukacin magoya bayanta, na ta kokarin ganin sun bata siyasar ta jihar Kano ta hanyar rungumar bangar siyasa a tarukanta, musamman ma a wannan lokaci da ake tunkarar zaben kananan hukumomi, lamarin da ta ce, babban ci baya ne ga demokradiyya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng