Wata jam'iyyar adawa ta bukaci a sake fasalin Najeriya, kowa yaci arzikin gidan su

Wata jam'iyyar adawa ta bukaci a sake fasalin Najeriya, kowa yaci arzikin gidan su

- Wata jam'iyyar adawa ta bukaci a sake fasalin Najeriya

- Jam'iyyar ta ce kowa yaci arzikin gidan su

- Shugaban sabuwar jam'iyyar ne dai mai suna Mista Kayode Arimoro ya bayyana hakan

Wata daya daga cikin jam'iyyun adawa sabbi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi wa rijista a kwanan nan mai suna Sustainable National Party (SNP) a turance ta bukaci da a sake fasalin kasar nan ta Najeriya.

Shugaban sabuwar jam'iyyar ne dai mai suna Mista Kayode Arimoro ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da ya kira a jiya ofishin jam'iyyar na Abuja.

Wata jam'iyyar adawa ta bukaci a sake fasalin Najeriya, kowa yaci arzikin gidan su
Wata jam'iyyar adawa ta bukaci a sake fasalin Najeriya, kowa yaci arzikin gidan su

KU KARANTA: An kashe wani babban dan siyasa a Kaduna

Legit.ng ta samu cewa Mista Kayode har ila yau ya bukaci a sake tsarin Najeriya ta yadda ko wace jiha zata habaka tattalin arzikin ta na cikin gida ta kuma ci abunta ba tare da ta raba arzikin da wata jihar ba.

A wani labarin kuma, A jiya ne dai wasu jiga jigan 'yan siyasar Najeriya daga jam'iyyu daban-daban suka marawa Cif Obasanjo baya wajen kaddamar da wata sabuwar kungiyar ceton 'yan Najeriya daga halin da suka shiga a garin Abekueta na jihar ogun.

Mun samu dai cewa a baya Cif Obasanjo din ya bayyana a cikin wata wasikar da ya aikawa shugaba Muhammadu Buhari cewa yana kira da a kafa irin wannan kungiyar da ba ruwanta da siyasa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng