Kayi murabus kawai, inji majalisar wakilan jihar Bunuwai ke gaya wa Ministan tsaro

Kayi murabus kawai, inji majalisar wakilan jihar Bunuwai ke gaya wa Ministan tsaro

- Kashe-kashen jihar Benue sun kai Intaha

- An kashe kauyawa kuma abin na ta zagayawa tsakanin kabilun jihar

- Ana dab da kisan kare dangi a wasu yankunan saboda kin jinin juna

Kayi murabus kawai, inji majalisar wakilan jihar Bunuwai ke gaya wa Ministan tsaro
Kayi murabus kawai, inji majalisar wakilan jihar Bunuwai ke gaya wa Ministan tsaro

Kashe-kashe da dauki dai-dai da kabilun jihar Benue ke yi wa juna ya kai intaha, inda kisa da ramuwar gayya ke ta zagayawa tsakanin manoma, makiyaya, kauyawa da ma masu wucewa a mota ta dazukan jihar, a kisa na rashin tausayi.

Majalisar jihar Benuwai cikin fushi a yau dinnan tayi kira ga Miniistan tsaro da ya gaggauta yayi murabus, tunda ya kasa kawo karshen kashe-kashen da ake yi a fadin jihar, wanda bashi da ko kan-gado, balle alamar shawo kansa.

DUBA WANNAN: Fulani na da damar zagawa koina a Najeriya,

Osinbajo ya gana da gwamnoni kan makiyaya da manoma

Kisan da ake a yankin, na rashin hankali ne, inda kowanne bangare kan kashe da sare kowa, ba babba ba yaro, babu mace babu namiji, abin ya kazannta sosai, kuma kamar ba wanda zai iya tsayar da shi, ya zuwa yanzu.

An dai caccaki shugaba Buhari kan kasa ko ziyartar jihar ta Benue, domin jaje ko ma bin kadi na me ke faruwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng