Fulani na da ikon zama a duk inda suke so a kasar nan
- Fulani 'yan kasa ne suna da ikon zama duk inda suke so
- An bukaci jihohin Binuwe da taraba su cire dokar hana kiwo
- Barazana ga fulani matsala ce babba
Hadin gwiwar kungiyoyi wanda ake yiwa lakabi da “Right Without Violence” sunce barazanar da ake yiwa Fulani makiyaya akan wuraren kiwon su matsala ce babba ga al’umma, kuma zai kara kawo rarrabuwar kan al’umma. Shugaban kungiyar, Dr. Ahmed Jibril, ya ba da sanarwar a ranar Alhamis a Zaria, inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.
DUBA WANNAN:
Yace, “Rayuwar al’umma na cikin matsala, ba zamu zauna mu zuba ido ba, ba tare da neman kariya ba, dole ne gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa don hana zubar da jinni a kasar nan. Sannan kuma Fulani cikkakun ‘yan kasa ne, suna da damar da zasu je ko ina su zauna a Najeriya.
“Ba zamu bar Najeriya ta zama kamar kasar Rwanda, Burundi ko Liberia ba, inda kabilanci ya jefa su a cikin rikice – rikice. Hana kiwo da jihar Binuwe da Taraba suka yi abu ne mai hatsarin gaske, sannan kuma hakan ya karya dokar kasa. Sannan abinda ya faru a jihohin ya faru ne saboda sakacin gwamnatin jahohin.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta binciko wadanda suka yi ta’asar domin hukunta su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng