Sunduki makare da kayan sojoji da makamai ya bace a tashar jirgin ruwan Najeriya
- Sunduki makare da kayan sojoji da makamai ya bace a tashar jirgin ruwan Najeriya
- Tuni dai kamar yadda muka samu kwamishinan 'yan sanda ya umurci a bi sahun sundukin
- Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan tashe tashen hankula tare da kashe-kashe
Yanzu haka ana zaman dar-dar da rashin tabbas a tashar jirgin ruwa mallakar gwamnatin tarayyar Najeriya dake a garin Apapa ta jihar Legas bayan da wani sunduki dauke da kayan sojoji da kuma makamai yayi batan dabo.
KU KARANTA: NAFDAC ta kama babban mai safarar kwayoyi a Gombe
Tuni dai kamar yadda muka samu kwamishinan 'yan sandan Najeriya dake a jihar Legas Mista Celestine Okoye har ya umurci sadaukan rundunar sa da su bi sahun sundukin tare da kamo wanda ya shigo da shi a cikin kwana daya.
Legit.ng ta samu dai cewa wannan abun al'al'ajabin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kasar musamman ma a yankin arewa ta tsakiya ta yi fama da tashe tashen hankula tare da kashe-kashe tsakanin makiyaya da kuma manoma.
A wani labarin, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya wajabta bin kadin sisi-da-kwabon da suka shiga dukkan daukacin ma'aikatun dake kasar nan ga ministocin sa a yayin taron tattaunawar da suke yi na mako-mako.
Kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu dai tun a makon da ya gabata ne a taron na majalisar zartarwar kasar suka fara yin bayanan a lokacin taron.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng